ABNA24 : Janar Qaanin ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi inda ya ce dukkanin ihu bayan harin da makiyan Iran suke yi don wani kokari ne kawai na dakile irin ci gaban da Iran take samu a fagage daban-daban musamman a fagen tsaron kasar musamman batun shirin makamai masu linzamin da Iran take da shi don kare kanta, yana mai cewa yanzu lokacin da makiya za su kawo wa Iran hari su sha ya riga da ya wuce.
Babban kwamandan rundunar ta Qudus ta IRGC yayi ishara da yadda Amurka ta yi karen tsaye ga yarjejeniyar nukiliyan da Iran ta cimma da ita tare da wasu kasashen Turai yana mai cewa mutane irin wadannan ba su cancanci tattaunawa da kuma cimma yarjejeniya da su ba.
Janar Qaanin yana mayar da martani ne ga kalaman wasu kafafen watsa labaran Amurka da suke cewa wai mataimakin ministan harkokin wajen Iran Sayyed Abbas Araqchi yayi kokarin ganin ya gana da mashawartar zababben shugaban kasar Amurka Joe Biden don tattauanwa da su lamarin da tuni ma’aikatar harkokin wajen Iran din ta musanta.
342/